Sunday, 9 April 2017

Duk Dan Majalisar Da Ya Yi Yunkurin Tsige Buhari A Bakacin Kujerarsa, Cewar Sanata Kwankwaso


Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Sanata Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso yace duk dan majalisa da yake gani wuyansa ya isa yanka ya yi kuskuren kawo kudirin tsige shugaba Buhari, to zai tabbatar da cewa ya debo wutar gasa kansa.
Kwankwaso yace "muna da labarin akwai
daga cikin 'yan majalisar wakilai wasu 'yan siyasa dake majalisa masu shirin kawo kudirin tsige shugaban kasa, to ina mai
tabbatar masu da cewar kafin su tsige shugaban kasa to mune za mu yi maganinsu.
Kuma za su gane kurensu.

Kwankwaso ya kara da cewa "ba za mu bar wasu tsiraru gurbatattu su tuge mana bishiyar mu ba, wacce muka dasa da hannun mu, kuma muna mata bayi harsai ta haihu kuma muna kyautata zaton duk dan Nijeriya sai ya ci 'ya'yan wannan bishiyar".
Sanata Kwankwaso ya shaida hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a fadar shugaban kasa a gaban gungun 'yan jaridu bayan ganawar su da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon ministan tsaron, ya kara da cewar har yanzu yana kyautata zaton shugaban kasa Buhari zai fitar da kasar daga halin da jam'iyyar PDP ta jefa ta. Tsohon gwamnan ya kuma roki 'yan Nijeriya musamman 'yan jam'iyyar su ta APC mai mulki da su cigaba da marawa shugaban kasar baya da jam'iyayr APC don ganin sun yi nasara. Kana Kwankwaso ya roki 'yan kasar da su ci gaba da addu'o'in samun cikekken lafiya ga shugaban kasar don ganin ya yi nasara.

Muna Kira Ga Shugaba Buhari, Da Ya Gaggauta Sallamar Shugaban Hukumar Fitar Da Kayayyaki Ta Nijeriya, Mista Gbenga Kuye, Inji Matasan Arewa



An yi kira da babbar murya ga Shugaban kasa Muhammad Buhari da cikin gaggawa ya hanzarta sallamar Shugaban hukumar fitar da kayayyaki ta Nijeriya Mista Gbenga Kuye daga kan mukaminshi, biyo bayan Wa'adin shugabanci na shekaru hudu na shugaban sun rigaya sun kare tun a bara, sannan har yanzu yana kan kujerar tare da cigaba da yin zagon kasa ga muradun kasa.
Gamayyar kungiyoyin cigaban matasan yankin arewacin tarayyar Nijeriya ne sukayi wannan kiran, a yayin wani taron manema labarai na gaggawa da suka kira, Wanda ya gudana a Otel din Tervan dake garin Kaduna.
Da yake jawabi a yayin taron manema labaran, Shugaban Kungiyar cigaban matasan arewacin Nijeriya na kasa baki daya Alhaji Imrana Nas ya bayyana cewar kiran nasu ya zamo wajibi ne bisa ga la'akari da yadda al 'amura ke wakana a wannan ma'aikata da kuma kokarin yin karfa karfa akan kujerar shugabanci da Mists Gbenga yakeyi ,inda yayiwa Majalisar Tarayya karyar cewar ya shiga office ne a cikin shekarar 2013 alhali a shekarar 2012 ya shiga office kuma Wa'adin shugabancin shi ya kare tun a Watan Disambar Bara.
Matasan Arewan sun kara da cewar da akwai wasu mayan hukumomi biyu wadanda ke karkashin Ma'aikatar ciniki da kasuwanci wanda suka hada da hukumar sarrafa Sukari ta Tarayya NSDC da kuma hukumar fitar da iskar Gas OGEFZA wadanda tuni suka mika ragamar shugabancin hukumomin nasu ga manyan sakatarorin hukumar biyo bayan kammala wa'adin shugabancin su, amma Mista Gbenga Kuye yayi kunnen uwar shegu da dokar kasa, lallai ya kamata Baba Buhari ka dauki matakan da suka dace a kanshi, inji matasan.
Matasan Arewan sun c igaba da cewar a fili yake Mista Koye yana ha'inta da zalunci ga yankin Arewa, domin a shekaru hudu da suka gabata sau biyu ne kawai Gbenga ya ziyarci reshen hukumar dake Kano, wanda rashin halartar tashi ya haifar da gagarumar matsala wajen cigaban 'yan kasuwa da sauran ma'aikatan hukumar dake shiyyar inda yasa wannan shiyya ta tafka asara kuma da gangan ya aikata haka, hakanan Mista Koye ya soke lasisin kamfanin samarwa da fitar da kayayyakin amfaninn Gona ta SEBORE dake Melwa Yola Jihar Adamawa wanda hakan ya haifar da gagarumar asara ga kamfanin da kuma Jama'ar yankin.
Matasan Arewan sun kara da cewar ba suna sukan Gbenga Koye a matsayinshi na dan kudancin Nijeriya bane, saidai suna magana ne akan a tabbatar ana bin tsari da kuma dokokin kasa, Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya nadashi shugaban wannan hukumar a shekara ta 2012 domin yin shugabanci na tsawon shekaru hudu, saboda wa'adin shugabancin shi ya kare ne a ranar 24/12/16, sannan an nadashi ne domin yiwa kasa baki daya aiki, ba wani bangare na kasa ba, sai gashi yana cutar da yankin Arewa, ya zama wajibi Shugaba Buhari ya dauki matakan dakatar dashi.

Matar Da Ta Haifi Jarirai Hudu A Jihar Bauchi Na Neman Taimako


Assalamu Alaikum wannan mata mai suna HUZAIFATU wacce Allah ya albarkace ta da haihuwar Jarirai guda hudu a garin Chibiyayi karamar hukumar Zaki, dake jihar Bauchi ranar Juma'a 31/03/2017 suna bukatar taimako kasancewar mijin ba mai karfi bane.
Domin tun daga haihuwar har kawo yanzu Huzaifatu da jariranta suna kwance a Asibitin FMC Azare suna karbar magani.
Na ziyarce su jiya na gabatar musu da wani taimako amma har yanzu suna bukatar taimako wanda ya hada da kudin sayen magani, abinci mai gina jiki, madarar jarirai da sauransu.
Ana iya taimakawa ta hanyar Mahaifin jariran Malam Saidu Chibiyayi 08079750567
Sai kuma ni da na yi rubutun 08036802500
Ko kuma a ziyarce su a bangaren haihuwar dake FMC Azare.
Allah ya bada ikon taimakawa amin,
Ismail Muhammad Jauro
8th April 2017



Matasa A Garin Gwarzo Sun Koma Gandujiyya Bayan Sun Kone Hulunan Kwankwasiyya




Matasa A Garin Gwarzo Sun Koma Gandujiyya Bayan Sun Kone Hulunan Kwankwasiyya
Wasu Matasa a garin Gwarzo kenan, suka fita daga Kwankwasiyya, suka kona jajayen hulunansu. Suka karbi akidar Gandujiyya.

Duk Dan Majalisar Da Ya Yi Yunkurin Tsige Buhari A Bakacin Kujerarsa, Cewar Sanata Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Sanata Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso yace...