Thursday, 13 October 2016

Babban Daraktan Kamfanin Man Najeriya NNPC Ya Kai Ziyara Bauchi



Biyo bayan samun man fetur a yankin tafkin Chadi dake cikin Najaeriya, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sa kamfanin man fetur din kasar NNPC ya kara bincike a jihohin Bauchi da Gombe
Babban Daraktan kamfanin man Najeriya Dr. Maikanti Kachalla Baru ya kai ziyara fadar gwamnan Bauchi inda ya shaidawa gwmnan ya zo ne bisa ga umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari kan binciken neman man fatur a jihar da makwafciyarta, wato Gombe.
Da yake magana da manema labarai yace ziyararsa cika umurnin shugaban kasa ne. Zasu bude aikin binciken karkashin kasa domin tabbatar cewa akwai man fetur a yankin da ya hada da Bauchi da Gombe. Yace zasu yi aiki a yankin da suke kira Gongola Basin da kuma tafkin Chadi. A yankin tafkin Chadi sun samu mai.

An nada Shaykh Dr. Khalid Abubakar Aliyu a matsayin Babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna



An nada Shaykh Dr. Khalid Abubakar Aliyu (Secretary General Jama'atul Nasril Islam) a matsayin Babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna.

An yi wannan nadin ne bisa amincewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr. Muhammad Sa'ad Abubakar III, da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris.

Allah ya taya shi riko, ya sauke nauyin da ke kansa. Allah ya hada kan Musulmi, ya bamu lafiya da zama lafiya, amin.

Idan Alkalai Basu Tsare Gaskiya Ba Dimokradiya Zata Gurgunce




Mai magana a madadin hukumar DSS Abdullahi Garba yayi bayani akan kamun da jami'ansu suka yiwa wasu alkalai bakwai da suka hada da alkalan kotun kolin Najeriya guda biyu.
Abdullahi Garba yace sun samu tsabar kudi masu dimbin yawa a gidajen alkalan banda motoci masu karen tsada iri-iri.
Gwamnatin Najeriya ta kare diran mikiya da jami'an DSS suka yiwa alkalan da nuna cewa kariya ga kowane mai mukami bai shafi maganar bincike ba musamman irin wannan yaki da cin hanci da rashawa.
Jawabin gwamnatin martani ne ga furucin babban alkalin Najeriya da shugaban kungiyar lauyoyi wadanda suke ganin matakin da aka dauka akan alkalan abun takaici ne.

Bam da Ya Tarwatse A Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar



A yayinda aka soma sake jiki a Maiduguri sai gashi yau da safe wani bam ya tashi a wata tashar mota inda ya hallaka mutane biyar tare da jikata wasu.
Da misalin karfe takwas na safiyar yau ne wani bam ya tashi cikin garin Maiduguri a tashar motar Munadare da yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jikata wasu da dama.
Rahoton da kakain 'yansanda jihar Borno ya fitar DSP Victor Isoko ya tabbatar da mutuwar mutane biyar wasu biyar kuma suka samu raunuka. Duk mutanen biyar da suka mutu suna cikin wata mota ce kirar Gulf. Mata hudu da direban motar suka halaka.

Shi'a: An kashe mutum goma a Katsina




Rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun ce an kashe akalla mutum goma lokacin da 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a suke juyayin ranar Ashura.
Bayanan da BBC ta samu sun ce lamarin ya faru ne a garin Funtua, lokacin da 'yan sanda da sojoji suka yi yunkurin hana 'yan Shi'ar yin tattaki da suka saba yi duk shekara domin tunawa da ranar ta Ashura.

Na yanke hukunci kan takarar Buhari a 2019 — Aisha Buhari




Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce, ta riga ta yanke hukunci kan ko mijinta zai sake tsayawa takara a 2019.
A wata kebantacciyar hira da ta yi da BBC, Aisha Buhari, ta kara da cewa shugaba Buharin ya yi watsi da wasu 'ya'yan jam'iyyar APC wadanda suka sha wahala da mijin nata a lokacin gangamin yakin zabe.
Hajiya Aisha, ta ce lamarin ya sa ana samun rabuwar kawuna tsakanin 'yan jam'iyyar.
A cewarta, "Mutane da yawa sun fara rarraba kawunan 'yan jam'iyyar APC, kuma hakan yana kawo mana damuwa da yawa yanzu. Saboda suna ganin su suka yi wahala amma ba sa koina yau".
Ta kara da cewa, "Wadanda ba su yi wahala ba; wadanda ko katin zabe ba su da shi su suka zauna a kan mutane suke yin komai da komai. Abin da nake guje musu (su manyan APC) shi ne boren da mutum miliyan 15 za su yi".

Duk Dan Majalisar Da Ya Yi Yunkurin Tsige Buhari A Bakacin Kujerarsa, Cewar Sanata Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Sanata Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso yace...