Rahotanni daga jihar Katsina da ke
arewacin Najeriya sun ce an kashe akalla mutum goma lokacin da 'yan
kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a suke juyayin ranar
Ashura.
Bayanan da BBC ta samu sun ce lamarin ya faru ne a garin
Funtua, lokacin da 'yan sanda da sojoji suka yi yunkurin hana 'yan
Shi'ar yin tattaki da suka saba yi duk shekara domin tunawa da ranar ta
Ashura.Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya kirga gawarwakin mutum takwas.
Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.
Ya kara da cewa an jibge jami'an tsaro a kusa da wurin da suke yin tattakin domin hana su, yana mai cewa jami'an tsaron sun rika harba bindiga sama domin tsorata jama'a.
Da ma dai jihohin Kaduna da Kano da kuma Katsina sun hana 'yan Shi'a yin tattaki a wannan shekarar.
Hasali ma, jihar Kaduna ta haramta kungiyar saboda zarginta da keta dokoki da kuma tayar da zaune tsaye, zargin da suka musanta.
BBC Hausa






No comments:
Post a Comment