Gidan Jaridar Arewa insider ta shahara ne wajen kawo muku sahihan labarai da zarar ta auku.labarai cikin harshen Hausa daga Arewacin Nigeria
Thursday, 13 October 2016
Bam da Ya Tarwatse A Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar
A yayinda aka soma sake jiki a Maiduguri sai gashi yau da safe wani bam ya tashi a wata tashar mota inda ya hallaka mutane biyar tare da jikata wasu.
Da misalin karfe takwas na safiyar yau ne wani bam ya tashi cikin garin Maiduguri a tashar motar Munadare da yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jikata wasu da dama.
Rahoton da kakain 'yansanda jihar Borno ya fitar DSP Victor Isoko ya tabbatar da mutuwar mutane biyar wasu biyar kuma suka samu raunuka. Duk mutanen biyar da suka mutu suna cikin wata mota ce kirar Gulf. Mata hudu da direban motar suka halaka.
Wannan sabon hari shi ne baya bayan nan tun wani harin da aka kai kofar sakatariyar jihar a cikin Maidugurin wanda ya hallaka jami'an 'yansanda biyu.
Watanni hudu ke nan da babban hamsan sojoji ya bude hanyar wadda ta tashi daga Maiduguri zuwa garin Gamboru inda aka samu tashin bam din yau.
Saidai rahotanni daga asibitin koyaswa na Jami'ar Maidugur ya ce mutane bakwai ne suka halaka yayinda 15 suka jikata.
Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da mutuwar mutane biyar a tashar yayinda ban din ya tashi.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Duk Dan Majalisar Da Ya Yi Yunkurin Tsige Buhari A Bakacin Kujerarsa, Cewar Sanata Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Sanata Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso yace...
-
Mai magana a madadin hukumar DSS Abdullahi Garba yayi bayani akan kamun da jami'ansu suka yiwa wasu alkalai bakwai da suka hada...
-
Assalamu Alaikum wannan mata mai suna HUZAIFATU wacce Allah ya albarkace ta da haihuwar Jarirai guda hudu a garin Chibiyayi karamar h...
-
A yayinda aka soma sake jiki a Maiduguri sai gashi yau da safe wani bam ya tashi a wata tashar mota inda ya hallaka mutane biyar tare d...

No comments:
Post a Comment